Polaroid
Google69490f6862051cb8
google-site-verification: google69490f6862051cb8.htmlgoogle-site-verification: google69490f6862051cb8.htmlgoogle-site-verification: google69490f6862051cb8.htmlBasheer journalist sharfadi14

Basheer journalist sharfadi14.jpg6
Basheer journalist sharfadi 11 1
Maraba Da Zuwa Wannan
Shafi Mai Al-barka 1

☀ Zabi inda kake son shiga ☀
Menunks
→Home
→Akidojin Ahlussunnah
→Addinin musulunci (35)
→40 Hadith (50)
→Fadakarwa (120)
→Neman labarai (20)
→Shi'a Kafirci (50)
→Hadith (55)
→Khudubobi (24)
→Tarihin magabata (60)
→Raddi / Maida martani (99)
→Face book post (30)
→Monthly Archives (60)
→Tambaya da Amsa (20)
→Sahabban Annabi {s.aw} (50)
→Taskar maluman sunnah (25)
→Akidar Y'an Shi'a Dangane da Al'kur'ani
→Fassarar Usulussunnah (20)
→Sheik Ja'afar {Rahimahullah} (65)
→Sheik Abubakar Gumi {Rahimahullah} (30)
→Sheik Dr. Muhammad Sani R/Lemo
→Salafiyyah Network Nigeria (100)
→Adam Sani Abu-Umayrah (99)
→Salaf Ustaz (79)
→Malama Ummi Ahmad Katsina
→Malama Amina Saleh Mande
→Labarai (40)
→Nishadantarwa (10)
→Siyasar Nigeria (9)
→Vidio (33)
→Audio (66)
→Hotuna (120)
→Internet Cheat (90)
→Site Achieve
→Application (10)
→Games (8)
→About me (01)

Wannan shafin mallakarCoollogo com-1281358 3
Ne




SHAFI DON KARUWAR MUSULMI
{TA YAYA ZAKIYI WA MIJINKI BIYYAYA} ?(001)
.
Wallafar malama jamila mukhtar saleh.
.
**ABUBUWAN DA KE CIKIN LATTAFIN**,
1)GABATARWA
2)TARIHIN MAWALLAFIYAR
3)GODIYA
4)SADAUKARWA
5)MA'ANAR AURE
6)HIKIMAR AURE
7)HUKUNCIN YIN AURE
8)SIFFOFIN MATAR DAYA DA ZA'A AURA
9)MATAKAN NEMAN AURE A MUSULLUNCI
10) SHARUDDAN AURE
11)AUREN DA SHARI'A TA HARAMTA
12)WASANNI YAYI KWANCIYAR AURE
14)KWANCIYAR AURE
15)LADUBBAN JIMA'I
16)ABUBUWAN DA AKA HANA GURI SADUWA
17)WANKAN JANABA
18)SIFFAR WANKAN JANABA
19)SAKAMAKON WANKAN JANABA
20)HAKKIN MA'AURATA A JUNANSU
21) NAU'IN MATA
22) RAYUWAN MATA KAFIN MUSULUNCI
23)RAYUWAN MATA A MUSULUNCI
24) RAYUWAN "YA MACE
25) A MATSAYINKI NA "YA MACE YAKAMATA KI SIFFANTU DA WADANNAN SIFFOFIN 26)SUTURAN "YA MACE
27)TSAFTAR JIKI DANA MUHALLI DON SAMUN NATSUWAR MAZAJE
28)ABINDA KE SA NAMIJI YA FITARAN MATARSHI
29) WASU ABUBUBWA DA AKE SO NAMIJI YA DINGA YIWA MATARSHI
30)TARBIYYA
31)ZAMA DA MIJI
32)SHAWARA GA "YAN UWA MATA
33) KAMMALAWA
34) MANAZARTA.
WADANNAN ABUBUWAN SUKE CIKIN LATTAFIN ZAMU DINGA KAWU MUKU DA IZININ ALLAH DAFATAN ALLAH YATAI MAKE MU
YAKUMA AMFANAR DA YAN UWAN MU BAKI DAYA
ITA KUMA
MALAMA JAMILA MUKHTAR SALEH ALLAH YASAKA MATA DA ALHERIN SA YAKUMA KARA MATA KWARIN GWUIWA. AMEEN



TA YAYA ZAKI WA MIJIN KI BIYAYYA ? (002)
.
Wallafar jamila mukhtar saleh,
.
:):D:) GABATARWA :):):)
.
Dukkan yabo da godiyasun tabbata ga Allah (swt).
Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Annabi Muhammadu (saw) da sahabbansa, da duk wanda suka bisu da kyautatawa har zuwa ranar tashin Alkiyamah.
**** MANUFAH ****
HAkika wannan littafi na rubuta shine don ya amfanar da Al'ummar yan" uwanmu musulmai.
Wannan littafi in bai amfanar ba to ba zai cutar ba, ni dai manufata Alkhairi ga yan" uwa musulmai, don warware matsalolin ma'aurata, da kuma samun nasarar zaman aure; domin auri-saki yayi yawa; ko Allah zai kawu saukin hakan a kasarmu najeriya
Allah(swt) yayi gaskiya inda yake cewa :
"ya ku waadanda kukayi imani, ku kare kanku da na iyalan ku daga shiga wuta wadda makamashinta mutane ne da duwatsu. Akanta akwai mala'iku masu karfi, basu sabama Allah abinda ya umurce su,kuma suna aikata abinda ya umurce su."
muna rokon Allah (swt) ya yafe mana kura-kuranmu da mukeyi dare da rana, yabamu ikon cikawa da imani, amin.
Daga yar" uwarku maison cigaban Addinin musulunci.
JAMILA MUKHTAR SALEH KOFAR BAI, KATSINA
GSM NO 080 68540221.
NA fara rubuta littafin nan a shekara ta 2011, kuma na kammala shi 20/91433h. Wanda yayi daidai da 08/08/2012:



TA YAYA ZAKI WA MIJINKI BIYAYYA (003)
.
Wallafar jamila muktar saleh.
.
** TARIHIN MAWALLAFIYAR **
.
JAMILA MUKHTAR SALEH an haife ni a unguwar kafar bai a shekara 1989. An sanyani makarantar firamare ta kayalwa watau ( Ahamdu comassie modal science primary school) kadan daga cikin malaman mu sune malama bailkisu, malama Rukayya muhammad da sauransu, Allah yasakanya masu da aljannah firdausi, Ameen.
.
A shekara ta 2002 na samu nasarar shiga makarantar kwalejin yan mata dake katsina watau GOVT.GIRLS, COLLAGE KATSINA ( GGCK).
Kadan daga cikin malaman mu na wannan makaranta a wannan lokaci sune; mal. Jamilu, mal. Babangida, da sunransu Allah yasakama masu da Aljannah firdausi Ameen.
.
Nasamu wucewa zuwa kwalejin koyon harshen larabci da ilimin Addinin musulunci watau (ATC) a shekara 2006. Kadan daga cikin malaman mu na wannan makaranta sune; mal. Ashiru Bala yandaki,mal. Masa'udu, da sauransu.
.
Allah (SWT) yasaka masu da Aljannah firdausi Ameen.
.
Bayan kammala wannan makaranta ATC sai na samu aikin koyarwa a wata makarantar islamiyya mai suna TARBIYYATUL AULAD dake kofar bai a shekarar 2007. Kasantuwar makaranta ce mai son cigaban Addinin musulunci, kuma sunada kyawawan manufofi, kadan daga cikin irin manufofin wannan makarantar na cigaban Addinin musulunci sune;
.
1) Tarbiyyantar da dalibai a karkashin jagorancin AL'QUR'ANI DA HADISAN ANNABI SAW.
2) isar da sakon Allah kuma umurni da kyawanan ayyuka da kuma hani da munanan ayyuka, DAs.
A shekara 2011 nafara kokarin wallafa wani littafi dan takaitacce; domin isar da sako ko umurni Annabi (saw) da yake cewa
.
" BALLIGU ANNI WALAU AYA"
.
ma'ana (ku isar sakona ko da aya dayane ).
.
Na fara buga wannan littafi ne mai suna;
.
TA YAYA ZAKI WA MIJINKI BIYAYYA? na hausa da fatan zai amfani al'ummar musulmi baki daya.
.
In an samu kuskure a gyara mani manufa shine alkhairi, Allah yake shiryar da wanda ya so.



TA YAYA ZAKI WA MIJIN KI BIYAYYA ? (006)
.
Wallafar malama Jamila muktar sale.
.
3) HUKUNCIN YIN AURE
Aure muhimmin abu ne acikin shari'ar musulunci, musamman idan mukayi duba da cewar Addinin musulunci yayi tafiyan daidai da yadda Allah ya hallici dan adam, kuma shi dan adam mun sani yana bukatar saduwa tsakanin mace da namiji.
Hakika, malamai sun dabi'antar da dan adam a bisa halayensa zuwa ma'aunai guda hudu (4) abisa hukuncin aure;
a) halal;- aure yana zama halal idan bashi da sha'awa, baya bukatan haihuwa, amma zai iya biyama matarsa hakkinta.
b) wajibi;-aure yana zama wajibi ga mutumin da yasan yanada karfin sha'awa, wanda idan baiyi shi ba zai iya fadawa cikin zinace-zinace. Sannan zai iya daukar nauyin matan.
c) mustahabbi;- aure yana zama mustahabbi ga mutumin da yasan zai iya danne sha'awar sa ba zai yi zina ba, ko kuma ya zamanto zai iya yin aure da biyawa matarsa bukatar ta, da riketa ko kuma ya zamto sha'awa bata dame shiba amma yana son matar, domin Annabi yace "kuyi aure don ku hayayyafa don inyi alfahari da yawan al'ummata ranar alkiyamah" Ahmad ibn hambal ya ruwaito shi.
d) haramun;- aure yana zama haramun ne ga wanda baya iya biyawa matarsa bukatar ta.
Bukata ta kasu kashi biyu (2); akwai bukata ta sha'awar saduwa da bukata ta ciyarwa, tufatarwa, da muhalli, saboda fadar manzon Allah saw "ya ku taron matasa, wanda yasami iko acikin ku yayi aure; domin shi zai kiyaye ganin sa kuma ya kiyaye kansa daga zina". Bukhari da muslim suka ruwaito wannan hadith.
Sahabin Annabi, Abdullahi dan masa'ud yace " koda za 'ace kwana goma (10) ne suka rage mani arayuwata, sai na so yin aure don gudun kada in hadu da ubangijina ina gwauro (marar aure) "



TA YAYA ZAKI YI WA MIJINKI BIYAYYA?(007)
.
Wallafar malama Jamila muktar sale.
.
SIFFOFIN MATAR DA ZA'A AURA.
.
1) Mace mai son Addini da kamun kai, kuma mai kunya.
2) yar gidan mutunci, mai kyakkyawan dabi'a, saboda faden manzon Allah saw " Ana auren mace don abubuwa guda hudu 4:- kyawunta, dukiyanta, nasabanta, da addininta," sai yace "kuzabi ma'abuciyar addinin."
.
Bukhari da muslim suka ruwaito shi.
.
MATAKAN NEMAN AURE A MUSULUNCI
.
1) YA halarta namiji yaga matar da zai nemi aurenta.
2) sa'annan yanemi izinin yimata magana daga wurin iyayenta; domin su fahimci juna.
3) bayan iyaye sunyi bincike akansa sai su bashi lokaci da wurin da zasu rinka zaunawa domin fahintar junansu.
4) ya halarta su iyayen mace ko namiji su nema wa "ya"yansu wanda ya dace dasu idan bukatar hakan ta taso.
5) mace zata iya nuna wata alama ga wanda ta ke so ko ta furta masa cewa tana sonsa musamman ga (bazawara).
6) wani ko wasu suna iya ganin wata yarinya da ta dace da wani mutumin kirki su bashi shawarar ya neme ta.
7) ko kuma shi namijin yayi wa macen da yake so jirwaye mai kamar wanka, idan tana idda ko takaba, kamar yace, "ba mata irinki ke rasa mazajen aure ba", ko kuma yace " idan kin kammala iddah karki fara sanar da kowa sai ni".
.
SHADUDDAN AURE
.
Hakika aure baya kulluwa har sai ancika sharudda kamar haka:-
.
1- waliyi:- wannan shine majibinci al'amarin daya daga cikin ma'aurata watau (macen da za'a aura). Shine wanda zai iya zama mahaifi ko dan uwan mahaifi ko wanda akayiwa wasicci da shi, ko shugaba na musulunci da sauransu.
2- sadaki:- shina abinda ake bayarwa domin ya halatta wa ma'aurata kawunan su da zaman tare a rayuwansu, kuma sadaki zai iya zamowa daga kudi, ko wasu kaya, ko aikin kwadago a gona ko karatun Al'kur'ani zuwa wani zangon karatun. Zai iya zama dukiya mai yawa ko dan kadan; amma karancin sadaki yafi albarka kamar yanda yazo a hadisin Annabi swa.
3- siga:- shine furucin da manemin aure zaiyi na neman abashi auren "wance" sannan mahaifi ko waliyin matar ya furta mashi kalmomi da cewa ya yadda ya bayar da auren "yar sa mai suna "wance" ga "wane" sai shedu su shaida.
4- auna jini:- don a tabbatar da ba'a dauke da wata cutar zamani ko makamanci yan haka.



TA YAYA ZA KIYI WA MIJINKI BIYAYYA? (008)

7) AUREN DA SHARI'AH TA HARAMTA :-

1- AUREN MUTU'A :- shi ne auren wucin gadi na sati 1, ko wata guda 1, ko shekara daya 1 da sauransu.
Wannan nau'in aure, Annabi s.a.w ya hana yin shi, ma'ana ya haramta shi har sau uku 3, tun a yakin khaibar inda yace " huwa haramun !" huwa haramun!!" huwa haramun!!! Ila yaumil kiyamah"watau haramun ne shi, haramun ne shi, haramun ne shi, (auren mutu'a) har ranar alkiyamah saboda haka yanzu duniyar musulunci tayi ittifaki cewa " babu masu dabbaka wannan aure sai mabiya akidar SHI'A (Addinin mutanen farisa ).

2-AUREN SHIGARI::-
shi ne auren musanyen "ya "ya batare da sadaki ba, kamar kabani "yar ka in aura, ni kuma in baka "ya ta ka aura. Ba wani sadaki kawai

3- AUREN MUSHIRIKI KO MUSHIRIKA:-
wannan hadisai da Alkur'ani da ijima'in malaman sunnah sun haramta shi. Saboda fadan Allah s.w.a a inda yake cewa
" kar ku aura mushirika har sai ta musulunta"
sai kuma yace
" kar ku aura ma mushuriki har sai ya musulunta"
suratul bakara aya 220.

4- AUREN KARUWA:-
Har sai idan ta tuba daga karuwancin ta, to ana iya auren ta.

5- AUREN WANDA YAI HARAMA DA AIKIN HAJJI.

6- AUREN YAN UWA MATA NA TSATSO DAYA LOKACI GUDA.

7- AUREN MATAN DA MUTUM YA SAKE TA SAKI UKU.

8- AUREN DA AKA DAURA BATARE DA WALIYYI BA.

9- AUREN MUHARRAMI KO MUHARRAMA.

10- MUHARRAMAI TA FUSKAN NASABA SU NE :-

A- uwaye
B- "ya "ya
C- yan uwa
D- "ya "yan "yar uwa.

11-MUHARRAMA TAFUSKAN SURUKUTA SU NE :-

A-"ya "yan mata (agololi )
B- matar uba
C- matar kaka
D- uwayen mata
E- kakar mata
F- matayen "ya "ya na tsatso.

12-AUREN CIKIN IDDAH.



Koma saman shafi

→Labarai
1234...9899100»

Share|

Kaima shiga a tattauna da kai
* No boards.

Online: Guests: 2


→Ra'ayin jama'a game damu

 IDAN KANA BUKATAR A TALLATA MAKA HAJAR KA A WANNAN SHAFIN DA SAURAN SHAFUKAN MU KANA IYA TUNTUBAR MU TA WADANNAN HANYOYIN KAMAR HAKA:


Email: bjournalist55@hotmail.com

Phone No: 09035830253

Facebook: Basheer Journalist Sharfadi

Address: Ittihad Computer Centre,  No 92 Daneji Kano


MAI TALLA SHI KE DA RIBA


*Bayanan ka*
Browser din da ka hawo Mozilla

Kasar da kake

Adadin Maziyarta 725603

Adadin Wadanda Sukayi Comment 65691

A Wadanda Suka Shiga Tattaunawar Mu 54


Follow @bjournalist55
→Yi Adding Dina Ta Facebook
→Yi Like Na Dakarun Sunnah Page
→Yi Like Dina Ta Facebook

*Shafuka Masu Alaka Da Mu*

→Basheer Sharfadi wordpress
Basheer Sharfadi Blog Spot
UP
→Home

Basheer Journalist Sharfadi (Abu Hafsah)
ISLAMIC DATE
  • phpimg2.php?it&ic=yellow



  • Click to Sms
    Click to Call


    Basheer journalist sharfadi3
    Coollogo com-1281358